Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar PDP na Kasa, ya nada Alhaji Salisu Lawal Uli a matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar a Jihar Katsina, har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe.
Kafin PDP ta nada shi a matsayin, Uli na rike da mukamin Mataimakin Shugaban jam’iyyar a jihar.
Matakin na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyar, Umar M. Bature.
Nadin na shi kuma na zuwa ne bayan ajiye mukamin da Shugaban jam’iyyar, Salisu Majigiri ya yi, don neman kujerar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Mashi/Dutsi a zaben 2023 mai zuwa.
Kafin maye gurbin Salisu Majigiri, ya jagoranci ayyukan jam’iyyar a jihar har na tsawon shekaru bakwai.
Har ila yau, yana cikin ’yan takarar Gwamna da suka sha kaye a zaben fid-da gwani na jam’iyyar a hannun Sanata Yakubu Lado, amma ya samu damar komawa matsayin shugaban jam’iyyar.
Sai dai an maye gurbinsa don ya samu dama mayar da hankali kan takararsa ta majalisar wakilai.
Sanarwar ta ce: “Bayan zaben Salisu Y. Majigiri a Jihar Katsina, a matsayin dan takarar Majalisar Wakilai na jam’iyyarmu a zaben 2023 mai zuwa, Kwamitin Gudanarwa na Kasa a madadin Kwamitin Zartarwa na jam’iyyarmu ta kasa, bayan la’akari da muka yi an amince da nadin Alhaji Salisu Lawal Uli a matsayin shugaban jam’iyyarmu a Jihar Katsina.
“Yayin da muke taya ka murna kan sabon nadin da aka mata, muna baka kwarin gwiwar yin aiki bisa tsarin dimokradiyyar kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu ya tanada.”