✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta lashe zaben gwamnan Bauchi

Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi ya yi tazarce

Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben Gwamnan Jihar Bauchi a karo na biyu da kuri’u mafi rinjaye 525,280.

Jami’in tattara sakamakon zabe a Jihar Bauchi, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, Mukaddashin Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawaya ya bayyana dan takarar jam’iyar PDP, Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaben da kuri’a 525,280.

Gwamnan ya doke abokin takararsa, Sadique Baba Abubakar, na Jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 432,272, sai Sanata Halliru Dauda Jika na Jam’iyyar NNPP da ya samu kuri’a 60,496.

Ya ce yawan masu rajistar zabe 2,749,268, inda daga ciki aka tantance masu jefa kuri’a 1,058,381.

Kuri’ar da aka jefa aka amince da su 1,034,379, kuri’un da suka lalace 15,600 daga cikin kuri’u 1,049,600.