Reshen jam’iyyar PDP a jihar Edo ya kalubalanci tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomhole da ya yi bayani kan yadda ya kashe Naira biliyan 42 da ya ce ya kashe kan harkar tsaro lokacin yana mulkin jihar.
Sakataren Yada Labarai jam’iyyar, Chris Nehikhare yayin jawabi ga manema labarai ya ce tsohon gwamnan ba mutumin da al’ummar jihar za su kara amincewa da shi ba ne.
Ya ce, “A tsawon shekaru takwas da ya shafe a kan mulki, ya kashe sama da biliyan 42 a matsayin kudin samar da tsaro amma babu wani abin a-zo-a-gani.
“Kamata ya yi a ce yanzu Oshiomhole bayani yake wa al’ummar jihar kan yadda ya kashe kudadensu ba wai yaklin neman zabe ba, yanzu fa kan mage ya waye.
“Babban abin dariya ne mutumin da ya tsaya a nan ya sossoki dan takarar PDP kwatsam yau a wayi gari wai ya ce ya yi kuskure, wannan ya nuna karara cewa shi ba abin amincewa ba ne”, inji Chris.
To sai dai da yake mayar da martini ta bakin kakakinsa, Victor Oshioke, Oshiomhole ya musanta zargin.
“Obaseki ya fito ya fada mana abin da ya karba a cikin shekaru hudu sai a kwatanta da shekaru hudun farkon Oshiomhole”, inji Victor.
Kan batun neman afuwar mai gidan nasa kuwa, ya ce duk dan Adam dama yakan yi kuskure, don haka ba laifi ba ne don ya nemi gafarar jihar kan kawo musu dan takarar da bai dace ba a baya.