Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta dakatar da tsohon Sanatan Kano ta Arewa, Bello Hayatu Gwarzo.
Dakatarwar na kunshe ne a cikin wata wasika da Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Gwarzo, Sanusi Ibrahim da Sakataren Jam’iyyar, Idris Abdullahi Danbaba suka sanya wa hannu mai dauke da kwanan watan 20 ga Afrilu, 2021.
- Kungiyoyin Ingila sun janye aniyar shiga gasar Super League
- Za mu murkushe cutar zazzabin cizon sauro zuwa 2025 — WHO
A cewar wasikar, an dakatar da tsohon Sanatan sakamakon yin abubuwan da suka saba wa jam’iyya da ya yi, kuma an yi hakan ne bisa shawarar da kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar ya bayar.
Wasikar ta ce: “Sakamakon shawarar kwamitin ladabtarwa bisa zargin aikata abubuwan da suka saba wa jam’iyya da kuma gazawarka na bayyana a gaban kwamitin don ji daga gare ka, halayyarka ta saba da Sashi na 58(1) na Kundin Tsarin Mulkin PDP na 2017.
Saboda haka, kwamitin zartarwa na mazaba ya amince ya dakatar da kai daga dukkan al’amuran jam’iyya har tsawon wata shida (6)”.
Wasikar ta ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take.