Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya dakatar da ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu na ciki da na waje daga bayar da kowanne irin agaji har sai bayan kurar zabe ta lafa.
Fintiri ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Gwamnatin Jihar da ke birnin Yola.
Gwamnan ya ce yana zargin kungiyoyin da fakewa da bayar da kayan tallafi wajen sayen kuri’u a jihar.
Ya ce duk wanda aka kama yana fakewa da sayan kuri’u ta hanyar ba da kayan agaji zai fuskanci hukunci.
Ya yi godiya ga jama’ar Jihar Adamawa game da hadin kan da suka bayar wajen zabar jam’iyyar PDP a Zaben Shugaban Kasa da ya gudana ranar Asabar.
Kazalika, gwamna Fintiri ya bukaci su sake zabar jam’iyyar PDP a zaben gwamna da na ’yan Majalisar Jiha da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris.
Gwamna ya kirayi jama’a da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa an sanya matakan tsaro da za su bai wa al’ummar jihar kariya wajen ganin an gudanar da zaben cikin lumana.