✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP na zawarcin Obaseki bayan APC ta hana shi takara

Jam’iyyar PDP ta ce tana maraba da Gwamnan Edo Godwin Obaseki ya shigo domin neman takarar kujerarsa bayan jam’iyyarsa ta APC dakatar da shi. Kwamitin…

Jam’iyyar PDP ta ce tana maraba da Gwamnan Edo Godwin Obaseki ya shigo domin neman takarar kujerarsa bayan jam’iyyarsa ta APC dakatar da shi.

Kwamitin Tantance ‘yan takarar APC na kwamitin Farfesa John Ayuba ya hana Obaseki neman kujerar gwamna ne saboda wasu bambance-bambance a takardunsa.

Kafin nan gwamnan wanda ke zaman doya da manja da Shugaban Jam’iyyar Adams Oshiomhole ya yi zargin rashin adalci muddin Oshiomhole na da hannu a zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Bayan katar da shin, gwamnan Godwin Obaseki ya ce ba zai daukaka kara ko kalubalantar hukuncin ba. Wasu rahotanni sun ce magoya bayansa sun yi taron gaggawa kan matakin da za su dauka.

Sai dai kuma zuwa yanzu babu tabbacin ko gwamnan zai amsa tayin komawa PDPn da ke zawarcinsa don naman takara.

Wata majiya a PDP ta ce akwai yiwuwar gwamnan na Edo ya dawo cikinta don neman takara kasancewar ita ce kadai jam’iyyar da ta kafu a dukkan matakai.

“Ba za mu hana shi ba idan ya nemi dawowa cikinmu. Za mu karbe shi kamar sauran wadanda suka fice a baya, idan yana son yin takar karkashin jam’iyyarmu”, inji majiryar.

Sai dai majiyar ta ki yin bayani ba ko Obaseki na da damar shiga zaben fitar da gwanin PDP na ranakun 23 da 24 ga watan Yuni.

Tuni dai jam’iyyar PDP a jihar Edo ta kammala tantance ‘yan takararta uku karkashin Kwamitin Hon. Kingsley Chinda.

Masu neman tsayawa takarar da aka tantance su ne Gideon Ikhine, Ogbeide Ihama da kuma Kenneth Imansuangbon.

Akwai yiwuwar PDP a jihar Edo za ta yi kwatankwacin abin da ta yi a jihar Binuwai lokacin da Gwamnan Binuwai din Samuel Ortom ya sauya sheka daga APC ya koma PDPn.

A wancan lokaci PDP ta karbi Ortom wanda ya rasa tikitin takara yayin da yake takun saka da jigon APC a jiharsa George Akume.