Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano ta nuna tsananin mamakinta game da yunkurin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na kashe sama da Naira miliyan 500 wajen kawata gadar Kofar Ruwa.
PDP ta bayyana yunkurin a matsayin almubazzaranci da dukiyar Kanawa.
Cikin wata sanarwa da Shugaban Jam’iyyar, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai ranar Asabar, PDP ta ce yana da kyau su jawo hankalin al’ummar Kano kan kudaden.
Jam’iyyar ta ce duk da cewa aikin yana da tsada sosai, amma suna sane da cewa an fara aiwatar da shi ne tun ma kafin Majalisar Zartarwar Jihar ta amince da shi kuma ba ya cikin kasafin shekarar 2021 ko 2022.
PDP ta ce hakan laifi ne da zai iya jawowa a iya tsige Gwamnan, wanda ya kamata a yi takatsantsan tare da sa ido.
Sanarwar ta ce, “Muna kira ga ’yan kungiyoyin farar hula da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFCC da ICPC da su binciki wannan ta’asa ta rashin gaskiya da rikon amana.
“A bayyane yake cewa Gwamnan yana kan kashe kashen kudi domin kara durkusar da tattalin arzikin Jihar Kano kafin cikar wa’adinsa na biyu don mayar da Kano baya.”
“A matsayinmu na jam’iyyar adawa kuma ’yan Jihar Kano na gari, mun yi Allah wadai da wannan aika-aika tare da yin kira ga Majalisar Dokokin Jihar Kano da kungiyoyin farar hula da masu ruwa da tsaki da su yi watsi da wannan aiki domin kuwa zai kawowa tattalin arzikin Jihar Kano koma baya,” inji PDP.
Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe makudan kudade har Naira 525,455,750.00 domin kawata gadar ta Kofar Ruwa, wacce aka sanya wa sunan marigayi Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim.