Kakakin dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Festus Keyamo ya ce Kungiyar Malaman Jami’o’i a Najeriya (ASUU), na yajin aiki ne saboda yarjejeniyar da ta kulla da jam’iyyar adawa ta PDP lokacin tana mulkin kasar.
Keyamo ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da kafar watsa labarai ta Trust TV a shirin Siyasar Yau wato Daily Politics na ranar Litinin.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Ririta Jari A Kasuwanci
- Za mu kara yaukaka dangantaka tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa — Putin
A cewarsa, daga shekarar 1999 zuwa 2015 lokacin da PDP ta mulkin kafin ta mika wa APC, ASUU ta shiga yajin aiki sau 12 na kimanin tsawon kwanaki 900.
“Batun ASUU da ake magana, mene ne matsalar ASUU a yanzu?
“Ai batu ne na yarjejeniyar da suka kulla tsakaninsu da gwamnati PDP a 2009.
“Sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar cewa za su cika wa ASUU alkawari.
“Duba da irin gazawar gwamnati da har ta yarda ta kulla yarjejeniya da ASUU, sannan suka rattaba hannu da sharuddan cewa za su cika.
“Wannan ya sa ASUU ta tsunduma cikin yajin aiki kuma ya kamata a fada wa ‘yan Najeriya cewa, ASUU ba ta shiga yajin aiki ba saboda APC ta kulla yarjejeniya da su, PDP ce ta yi alkawari da su.
“Ba wai muna jingina matsalar ga wasu ba ne, kuma muna kokarin mu ga matsalar ta kau.
“Daga shekarar 1999 zuwa 2015 lokacin da PDP ta mulki kasar, ASUU ta shiga yajin aiki sau 12, wanda idan aka lissafa tsawon lokutan, za a ga cewa ta yi kwanaki 900 tana yajin aiki.”