Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dokta Isa Ali Pantami, ya magantu a kan ci gaba da isar da koken ’yan Najeriya game da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa musamman a Arewacin kasar.
Pantami, wanda babban malamin addinin Islama ne, ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan kisan wulankanci da ’yan Boko Haram suka yi wa wasu mutum 43 ranar Asabar a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin kasar.
- Harin Zabarmari: Buhari ya jajanta kan kisan manoma 43
- Boko Haram ta yi wa manoma 43 yankan rago a Borno
Dokta Pantami ya ce zai isar da sakon damuwar da al’ummar Najeriya ke ciki ga Shugaban Kasa game yankan rago da masu tayar da kayar bayan suka yi wa fiye da mutum 40 a jihar Borno.
Ministan ya ce zai yi hakan ne bayan wani mai amfani da shafin na Twitter, Boss Mustapha (@__yellows), ya roke shi da yin hakan.
Matashin mai amfani da sunan Boss Mustapha @__yellows a shafin na Twitter, ya hada Ministan da Allah a kan ya yi wa Shugaban Kasa magana domin a cewarsa kisan mutum fiye da 40 rigis ko da a shirin fim ne lamari ne mai firgitaswa.
A cewar matashin: “Ya Sheikh @DrIsaPantami – muna kawo kukan mu gareka. Dan Allah dan Annabi ka samu ka yi ma shugaban qasa magana.”
“Mutum arba’in da hudu (43) ko a movie aka kashe lokaci daya abun da ban tsoro. Dan Allah a taimaka a yi wani abun a kai abun ya fara yawa.”
Da ya ke mayar da martani, Dokta Pantami ya ce zai ci gaba da isar da sakon al’ummar Najeriya ga Shugaban Kasar kamar yadda ya saba tare da yin addu’a ga mamatan da aka kashe.
Ya wallafa cewa: “Muna yin hakan kuma za mu ci gaba da yi Insha Allah.”
“Zan isar masa da wannan sako kamar yadda na yi magana da Gwamna Zulum babu jima wa. Allah Madaukakin Sarki ya jikansu da rahama.”