Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Pantami, ya samo wanda zai biya miliyan 50 daga Naira miliyan 100 na kudin fansar sauran ’yan mata ’yan gida daya da ’yan bindiga suka sace a Abuja.
Aminiya ta ruwaito yaddaa daren Talata ’yan bindiga suka sace wani magidanci da ’ya’yansa mata shida a Karamar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya.
Daga bisani suka sako shi, suka nemi ya biya Naira miliyan 60 zuwa ranar Juma’a kafin su sako ’ya’yan nasa.
Zuwa ranar Juma’ar Naira miliyan 30 iyalan suka iya tarawa, amma ’yan ta’addan suka ki amincewa, suka kashe babbar ’yarsa, Nabeeha, wadda ke ajin karfe a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya
Daga nan suka kara kudin fansa zuwa miliyan 100, tare da barazanar kashe sauran ’yan uwanta idan har ba a biya ba.
A kan haka ne tsohon minista Isa Pantami ya bayyana cewa ya tattauna da “aboki kuma dan uwa” wanda zai biya Naira miliyan 50 daga kudin fansar ragowar ’yan matan.
Ya rubuta cewa, “Duk da cewa ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga ’yan bindiga, amma ya zama dole, tunda ta tabbata jiya mun rasa ’yarmu Nabeeha, kuma ana barazanar kashe sauran ’yan uwanta biyar, kamar yadda mahaifinsu ya shaida min.
“Na yi magana da da wani abokina kuma dan uwa wanda ya ce zai biya Naira miliyan 50 …. duk wanda ke da hali zai iya karawa domin mahaifin ya samu abin biya ya ceto rayuwar ’ya’yan namu.”
Ya kuma yi addu’ar zaman lafiya a kasar, ya kuma jajanta wa iyalan dalibar da aka kashe tare da yi addu’ar Allaha Ya saka wa wadanda suka rasu, Ya sanya su a Aljanna.