Shahararren dan kwallon kulob din Arsenal na Ingila Mesut Ozil ya gindaya wa kulob din wadansu sharudda kafin ya amince ya ci gaba da zama a kulob din.
dan kwallon ya ce muddin kulob din ana so ya ci gaba da zama a kulob din to sai an mayar masa da rigar kwallo mai lamba 10 wacce Jack Wilshere yake amfani da ita maimakon mai lamba 11 da yake amfani da ita a halin yanzu. Ya ce yin haka ko shakka babu zai kara masa kwarin gwiwar ci gaba da zama a kulob din ba tare da tunajin canza sheka ba.
Mesut, wanda kwantaraginsa za ta kare da kulob din a karshen kakar wasa ta bana, ya ce daya daga cikin sharuddan da zai sa ya ci gaba da zama a kulob din shi ne a canza masa rigar kwallonsa ta koma Lamba 10 maimakon lamba 11 da yake amfani da ita a halin yanzu. Sannan dan kwallon ya bukaci a kara masa albashi daga Fam dubu 150 kwatankwacin Naira Miliyan 71 a duk mako da yake karba a halin yanzu.
Wadannan na daga cikin dalilan da suka sa Ozil din ya ki sabunta kwantaraginsa a kulob din kawo yanzu, sai dai koci Arsene Wenger ya ce zai yi duk maiyiwuwa ya ga am biya wa dan kwallon bukatunsa kafin karshen kakar wasa ta bana. Hakan ya nuna kocin ya sha alwashin biya wa dan kwallon duk bukatunsa don ganin ya sabunta kwantaraginsa a kulob din.
Mesut Ozil dai ya sayi katafaren gida a birnin Landan da hakan ya nuna yana da sha’awar ci gaba da zama a kulob din Arsenal. Sai dai kawo yanzu rahotanni sun nuna Jack Wilshere bai amince da tayin mika wa Ozil rigar kwallonsa mai lamba 10 ba.