’Yan Najeriya da dama za su jima ba su mance zaben Gwamnan da aka gudanar a jihar Osun a 2018 ba, wanda a karon farko tun bayan dawowar kasar tsarin Dimokuradiyya, aka bayyana zaben Gwamnan wata jiha a matsayin wanda bai kammala ba, ko inconclusive a Turance.
Zaben, wanda aka gudanar da shi ranar 23 ga watan Satumban 2018, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana shi ne a matsayin inconclusive, bayan an kammala tattara sakamakon ilahirin Kananan Hukumomin Jihar guda 30.
- Yadda rashin tsaro ke barazana ga Zaben 2023 a Arewa
- Ina umartar dakarun Najeriya da su shafe ’yan ta’adda daga doron kasa —Buhari
A bana ma, Asabar, 16 ga watan Yulin 2022, ita ce ranar da mutanen jihar ta Osun za su sake fita rumfunan zaben sabon Gwamnan da zai ja ragamar jihar daga bana har zuwa shekarar 2026.
A wancan zaben na 2018 dai, INEC ta yi wukar kugu da cewa yawan kuri’un da aka soke sun haura tazarar da ke tsakanin ’yan takara biyu da ke kan gaba a zaben – Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP da kuma Gboyega Oyetola na APC.
A cewar baturen zaben na wancan lokacin, kuma Shugaban Jami’ar Fasaha da ke Akure, Joseph Fuwape, dan takarar PDP ya sami kuri’a 254,698, yayin da na APC ya sami kuri’a 254,345.
Sai dai an soke kuri’a 3,498, yayin da tazarar da ke tsakaninsu ba ta wuce ta kuri’a 354 ba.
Hukumar dai ta ce ta yi la’akari ne da tanade-tanaden sashe na 153 na Dokar Zabe ta Kasa, wajen daukar matakin.
Hakan ta sa INEC ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, sannan ta sanya ranar Alhamis, 27 ga watan Satumban 2018 a matsayin ranar kammala shi.
Sai dai a ranar zagaye na biyu na zaben, kusan ilahirin jiga-jigan APC na Najeriya sun yi wa jihar tsinke, kafin daga bisani INEC ta ayyana dan takarar na APC, Gboyega Oyetola a matsayin wanda ya lashe shi, sabanin na PDP da yake kan gaba a zagayen farko, kuma aka yi hasashen shi zai iya lashewa.
Lamarin dai a wancan lokacin ya jawo cece-kuce daga ’yan Najeriya da ma musamman jam’iyun adawa da ke ganin jam’iyyar APC mai mulki ta bullo da salon ne don yin magudi a je zagaye na biyu, a duk inda ta ga alamun ba za ta kai labari ba.
Sai dai INEC ta sha musanta wadannan zarge-zargen, inda ta ce babu ruwanta da haka, hasalima abin da ta yi ba sabo ba ne a Dokar Zabe.
Da babban zaben 2019 ya zo, an sami jihohi da dama, irin su Kano da Sakkwato da Bauchi da Bayelsa, wadanda INEC su ma ta ayyana zaben gwamnoninsu a matsayin inconclusive.
A bana ma a jihar ta Osun, akwai jam’iyyu da dama da suke fafatawa a zaben, kodayake takarar za ta fi zafi ne tsakanin Gwamna mai ci, Gboyega Isiaka Oyetola, na jam’iyyar APC, da kuma Adeleke Nuruddeen Oyetola na PDP.
Ana ganin zaben na jihar Osun a matsayin wani zakaran gwajin dafin babban zaben 2023 da ke tafe.
Sai dai babban abin jira a gani shi ne ko tarihin inconclusive irin na 2018 zai sake maimaita kansa a jihar? Lokaci ne kawai zai nuna hakan.