Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari na daga cikin manyan bakin da za su halarci bikin mika sanda ga Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Za a gudanar da taron bikin ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano, a ranar Asabar, 3 ga watan Yuli, 2021.
- Tsohon Sakataren Tsaron Amurka Donald Rumsfeld ya mutu
- ’Yan bindiga sun kai wa ayarin Ganduje farmaki a hanyar Zamfara
Aminu Bayero ya zama Sarkin Kano na 15 daga Gidan Sarautar Fulani na Masarautar Kano a ranar 9 ga watan Maris, 2020 bayan sauke Muhammadu Sanusi II da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi.
Da yake zantawa da manema labarai, Dan-Dalan Kano, Abbas Dalhatu, ya ce za a samar da cikakken tsaro don tabbatar da an tashi lafiya daga taron.
Ya ce za a girke jami’an tsaro 4,000 da suka hada da DSS, sojoji, jami’an Civil Defense da sauran jami’an tsaro, a yayin bikin.
A cewarsa, daga cikin mutum 16,000 da za su halarci bikin, an ware kujeru 3,000 ga manyan baki, ragowar kujeru 13,000 kuma ga sauran mahalarta.
Dalhatu, ya bayyana cewa an nada marigayi Alhaji Ado Bayero sarautar Kano a Filin Wasa na Sani Abacha shekara 53 da suka gabata, kuma wannan karon ma za a nada magajin nasa a filin wasan.
“Baki da dama za su halarci bikin ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.”
Ya ce jim kadan bayan kammala mika sandar, za a yi hawa na musamman don kawata bikin, sannan Sarki zai zaga cikin gari don gaisawa da jama’a.
“A ranar Litinin, Sarki zai zaga cikin gari a kan dokinsa don gaisawa da jama’a, zagayen zai fara daga Fadar Sarki zuwa unguwar Fagge, Sabon Gari daga nan kuma ya sake dawowa fada.”
Kazalika, Aminiya ta ruwaito Madakin Kano, Alhaji Nabahani Ibrahim yana cewa, za a shafe kwanaki biyar ana bikin mika sandar ga Sarki Aminu da ya fito daga tsatson Gidan Fulani na Masarautar Dabo.
Alhaji Nabahani wanda ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, ya ce za a fara gudanar da bikin ne da wata lacca tun a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli, sannan a karkare da hawan Durba a ranar Litinin, 5 ga watan na Yuli.
A cewarsa, “Tsohon Shugaban Jami’ar Karatu daga Gida ta Kasa (NOUN), Farfesa Abdallah Uba Adamu ne zai gabatar da laccar mai taken ‘Masarautar Kano a Jiya, Yau da Gobe’, a dandalin bikin yaye dalibai ta Jami’ar Bayero da ke Kano”.