Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya daura wa sabon Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba sabon mukaminsa.
Osinbajo ya daura masa sabaon mukamin nasa ne wani karamin biki a Fadar Shugaban Kasa tare da Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi a ranar Laraba.
A ranar Talata Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin DIG Alkali a kujerar, ta bakin Dingyadi da cewa nadin ya fara aiki ne nan take.
Alkali zai maye gurbin Mohammed Adamu, wanda wa’adinsa ya cika wa ranar 1 ga Fabrairu, 2021, amma aka yi masa karin wata uku; sai dai kuma kwana uku kafin cikar sabon wa’adin aka maye gurbinsa.
Wane ne IGP Alkali?
Kafin zaman Sufeto Janar, shi ne Mataimakin Sufeto Janarn Mai Kula da Binciken Manyan Laifuka a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda da ke Abuja.
Ya fara aikin dan sanda ne a shekarar 1988, bayan kammala kammala karatun digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) a 1985.
Kafin digirinsa na fakro, Alkali na da shaidar malumta ta TC II daga Kwalejin Horas da Malamai da ke Potiskum, Jihar Yobe a 1980.
A yayin da yake aikin dan sanda, ya karo karatu, inda ya yi digirinsa na biyu a fannin Gudanarwar (MPA) a Jami’ar Maiduguri a 1997.
Burinsa na aikin dan sanda shi ne: inganta aikin ta hanyar samar da kayan aiki da tara bayanan sirri, ba da kwarin gwiwa da jagoranci na gari da kuma kwarewa da nufin inganta yanayin tsaro ta hanyoyin zamani da kuma fahimta da yarda tsakanin ’yan sanda da al’umms bisa bin dokar kasa.”