✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Osinbajo ya dakatar da rushe Fadar Masarautar Agege

Al’ummar garin Agege sun kasance cikin farin ciki, bayan samun tabbaci daga Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na dakatar da rushe Fadar Masarautar Agege…

Al’ummar garin Agege sun kasance cikin farin ciki, bayan samun tabbaci daga Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na dakatar da rushe Fadar Masarautar Agege da Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya ke dab da yi.

Mataimakin Shugaban Kasar ya ba da tabbacin ne lokacin ziyarar da ya kai wa al’ummar Arewa mazauna Legas a fadar Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Muhammadu Musa Dogonkadai a ranar Lahadin da ta gabata bayan da Majalisar Sarkin Agege ta bayyana masa halin da take ciki na rashin tabbas game da umarnin da Hukumar Jiragen Kasa ta bayar na rushe fadar.

Yunkurin wanda aka bayyana a matsayin dalilin ayyukanta da suka ratso ta bangaren fadar, masarautar ta Agege ta roki Mataimakin Shugaban Kasar ya sanya baki domin a jinkirta rushe fadar kuma gwamnanti ta bai wa masarautar sabon wurin da za ta gina sabuwar fada ta dindindin, lamarin da Mataimakin Shugaban Kasa ya amsa, ya kuma yi alkawarin yi wa mahukuntan hukumar jiragen kasar magana.

Tunda farko Kakakin Masarautar Agege, Alhaji Kabir Dinar ya karanto wa Farfesa Osinbajo tarihin masarautar wacce ita ce masarauta Hausawa mafi girma da tsufa a daukacin jihohin Kurmi. Daga nan Mataimakin Shugaban Kasar ya nemi a fada masa bukatun al’ummar Arewa mazauna garin Agege, inda aka bayyana masa cewa akwai tarin matasa da suka kammala karatu wadanda ba su da aikin yi, kuma akwai mata da sauran jama’a da suke bukatar a sanya su a tsarin tallafin da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa. Nan take Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na da tarin wadannan tsare-tsare kuma da sannun za a fadada su ta yadda al’ummar Agegen za su amfana.

Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana farin cikinsa bisa ziyarar da ya kai wa Sarkin Hausawan yana mai cewa ya san Sarkin da dadewa a lokacin da yake aiki a matsayin Ministan Shari’a na Jihar Legas.

A nasa bangaren, Mai martaba Sarkin Hausawan Agege ya karamma Mataimakin Shugaban Kasar, inda ya ba shi kyautar babbar riga da ta sha aiki da ’yar ciki da wando irin na sarakuna.