✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Osinbajo bai kamu da cutar Coronavirus ba

Sakamakon gwajin da aka yi wa mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya nuna ba ya dauke da cutar coronavirus. Mai taimaka wa Osinbajo, kan…

Sakamakon gwajin da aka yi wa mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya nuna ba ya dauke da cutar coronavirus.

Mai taimaka wa Osinbajo, kan yada labarai, Laolu Akande ya sanar da hakan bayan amsa sakonnin da aka tura masa kan matsayin alakar da mataimakin Shugaban ya yi da wasu da aka sanar sun harbu da cutar.

Laolu Akande, ya sanar da hakan ne yau Laraba. Ya wallafa cewa mataimakin shugaban na killace kansa kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta nuna.