✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ooni na Ife ya zama dan fim a Hollywood

Sarkin dai ya kasance abin labari a watannin baya, inda cikin dan lokaci ya auri mata sama da goma, bayan ya sake zama gwauro

Ooni na Ife Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya fito a wani fim din masana’antar Hollywood ta kasar Amurka a karon farko.

Sarkin dai ya kasance abin labari a watannin baya, inda cikin dan lokaci ya auri mata sama da goma, bayan ya sake zama gwauro — batun da ya tayar da kura, musamman a kafofin sada zumunta.

A fim din da ya fito mai suna ‘Take Me Home’, Oba Adeyeye Ogunwusi ya fito ne a matsayinsa na asali, wato Ooni na Ife, wanda ake tunanin zai kayatar da masu kallo.

Fim din ‘Take Me Home’ wanda Ooni na Ife ya fito a ciki, ya yi kokarin fito da abubuwan tarihi na asali.

An gina shi ne a kan labarin wata yarinya Ba’amurkiya wadda donanni suka shige ta bayan ta sanya kayan wasu dodannin Afirka da ’yan yawon bude ido suka sace a garin Ile-Ife.

A kokarin ceto rayuwar yarinyar ce iyalanta suka samu wasu ’yan Afirka mazauna Amurka da suka yi musu kwantance, suka kamo hanya kacokam dinsu, suka yi tafiyar da ta jefa su cikin halin tsaka-mai-wuya.

A matsayinsa na shugaba kuma jagoran Yarabawa da addininsu na gargajiyar, Ooni na Ife ne ke da alhakin rokon dodannin nasu a  Òrìṣà.

A cikin fim din, Ooni na Ife ya bayyana irin al’adun al’ummar Yarabawa da kuma muhimmancinsu ga Yammacin Duniya.

Masanin tarihi kuma furodusa, Dotun Taylor, ne ya shirya fim din  ‘Take Me Home’.

Jaruman Hollywood da suka fito a ciki sun hada da Dave Sheridan da Amber Rivette da Felissa Rose da Meji Black.

Sai kuma ’yan Nollywood irin su Abdullateef Adedimeji da Bayo Bankole (Boy Alinco na fim din Papa Ajasco) da sauransu.