Rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo ta ce ta kama mutum takwas masu alaƙa da shirya taron da ya janyo turmutsutsu a wata makaranta a ranar Laraba, ciki har da tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Naomi Agunwusi da Shugaban makarantar Fasasi Abdulahi da wasu mutum shida.
Rahotanni sun ce tsohuwar mai ɗaƙin Sarki Ooni na Ife, Naomi Silekunola Ogunwusi ce dai ke shirya wannan taron bikin na al’ada a duk shekara inda musamman yara ke haɗuwa lokacin hutu su yi wasanni.
- Zargin N110.4bn: Kotu ta bada belin Yahaya Bello kan N500m
- Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N899
Rundunar ta bayyana cewa an samu ƙarin gawarwaki ƙananan yara da ya kai 35 sannan guda shida suna cikin mummunan yanayi a asibitoci daban-daban.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Alhamis, daga Jami’n Hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso ya fitar.
Tun bayan mummunan turmutsutsu da aka samu a wata makarantar Islamiyya a Basorun da ke birnin Ibadan.
An dai ware wajen taron da zai ɗauki adadin yara mahalarta 500, amma sai aka gano cewa sama da yara 7,500 ne suka halarci taron.
Ana dai nuna yatsa ga tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Naomi Silekunola Ogunwusi da mai gidan rediyon Agidigbo FM, Oriyomi Hamzat waɗanda su ne ake yi wa kallon da haddasa al’amarin.
A cewar Rundunar ‘yan sandan jihar waɗanda aka tsare sun haɗa da Genesis Christopher mai shekara 24 da Tanimowo Moruf mai shekara 52; da Anisolaja Olabode mai shekara 42; da Idowu Ibrahim mai shekara 35; da kuma Abiola Oluwatimilehin mai shekara 25.
Zuwa yanzu dai yara 35 ne suka rasu yayin da wasu shida ke cikin mummunan yanayi a asibitocin jihar.