✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Omicron ya fi yawa a kasashen Afrika —WHO

WHO ta bayyana cewa adadin wadanda suka harbu da Omicron ya fi yawa a Afirka

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ce samfurin cutar COVID-19 na Omicron ya fi yawa a nahiyar Afrika, fiye da sauran nahiyoyin duniya.

Kasashen Afrika 10 na dauke da kashi 46 na mutanen da suka harbu da sabon samfurin cutar na Omicron.

WHO ta ce kwayar cuta ta fi yaduwa a kasashen Kudancin Afrika, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Sai dai masana na kara sa ido kan karuwar masu harbuwa da cutar da ita kanta kwayar cutar domin gano yadda tasirinta yake a jikin dan Adam.

Binciken WHO ya tabbatar da cewa wadanda ke kwance a asibiti ko cibiyoyin killace mutane ba su da yawa.

WHO ta yi gargadin cewa hana shigar baki wasu kasashe ba zai hana yaduwar cutar ba.

Amma ta shawarci mutane da su mayar da hankali wajen karbar rigakafinta, wanda shi ne kadai zai rage tasirinta.

A wannan satin da muke ciki, kasashen Birtaniya da Saudiyya suka hana baki daga Najeriya shiga kasashensu a sakamakon bullar kwayar cutar ta Omicron.

Tuni jama’a musamman masu zuwa Saudiyya don gudanar da ibada suka shiga bayyana rashin jin dadinsu kan matakin da mahukunta kasar suka dauka.

%d bloggers like this: