✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Omicron ta kashe mutum na farko a Birtaniya

Mutum na farko ya rasu bayan harbuwa da kwayar Omicron ta cutar COVID-19 a Birtaniya.

Mutum na farko ya rasu bayan harbuwa da kwayar cutar COVID-19 nau’in Omicron a kasar Birtaniya.

Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson ya sanar da hakan ne a ranar Litinin, yana mai kira ga mutanen kasar da su karbi allurar rigakafin COVID-19 domin dakile yaduwar cutar.

Ya ce, Omicron na “kwantar da mutane a asibiti” kuma “an tabbatar da mutuwar kalla mutum daya,” yana mai bukatar jam’ar kasar su yi watsi da masu cewa Omicron ba shi da wani karfi sosai.

Fira Minista Boris Johnson ya ce abin da ya fi dacewa shi ne mutane su je su karbi karin “allurar cutar,” su yi wasti da wadancan maganganu.

Kawo yanzu kashi 40 cikin 100 da masu cutar COVID-19 a Birtaniya suna dauke ne da kwayar Omicron.

Jama’ar kasar dai na ta tururuwar zuwa cibiyoyin karbar allurar rigakafin cutar, inda aka ware ranar Juma’a ga masu shekara 30 zuwa 39.