✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Okonjo-Iweala: Yadda Amurka za ta bata wa WTO lissafi

Kasashe 104 sun goyi bayan Okonjo-Iweala amma Amurka ta ce allambaran sai ’yar takarta

A ranar Laraba Amurka ta yi kafar ungulu bayan komai na tafiya babu tangarda a yunkurin tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala na zama sabuwar Darakta-Janar ta Cibiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO).

Bayan zaman Babban Zauren WTO, an ambato Shugaban Zauren, David Walker na cewa Okonjo-Iweala ce alamu suka nuna ta fi damar goyon bayan daukacin mambobi domin darewa kujerar.

Amma daga bisani Amurka ta yi tutsu ga zabin Okonjo-Iweala wadda ke neman zama mace ta farko da ta shugabanci cibiyar.

Kafin matakin na Amurka, Kakakin WTO, Keith Rockwell, ta ce “’Yar takara mafi samun amincewar dukkannin mambobi it ace Dakta Ngozi Okonjo-Iweala daga Najeriya. Nan gaba za a tattauna kan abu na gaba”, kamar yadda ta ruwaito Mista Walker na cewa.

Gabanin nan, goyon bayan manyan jami’an WTO a Hedikwatarta da ke birnin Geneva na kasar Switzerland da tsohuwar Ministar Kudin ta Najeriya ta samu ya ba ta karin rinjaye a kan abokiyar hamayyarta, Mis Yoo Myung-hee ta kasar Koriya ta Kudu.

Akalla kasashe 104 ne ciki har da Faransa, Jamus da wasu manyan kasashen Turai suka bayyana goyon bayan nadin ’yar Najeriyar.

Duk da haka Babban Zauren WTO ya ce za a ci gaba da tattaunawa da kasashe kan abin da zai faru, gabanin zaben da ke tafe a ranar 9 ga Nuwamba kafin nadin sabon Darakta-Janar din a daidai lokacin da cibiyar ke cika shekara 25 da kafuwa.

A wani abu mai kama da mi’ara koma baya, Mataimakin Wakilin Amurka, Dennis Shea, ya ki amincewa da zabin Ngozi ta zama’yar takara tilo babu hamayya.

Shea, ya shaida wa zaman wakilan WTO a Geneva cewa Amurkawa ba su amince ba da yadda aka yi zabin.

A sanarwarsa, Ofishin Wakilin Amurka kan Kasuwanci (USTR) ta bukaci a zabi Ministar Kasuncin Koriya ta Kudu, Yoo Myung-hee ta zama sabuwar Darakta-Janar na WTO.

“Minista Yoo cikakkiyar kwararriya a fannin kasuwanci ce da ta shekara 25 tana aiki a matsayin mai shiga tsakani a kasuwani kuma mai shirya tsare-tsare.

“Tana da duk kwarewar da ake da bukata na zama managarciyar shugaba a cibiyar.

“Wannan mawuyacin hali ne ga WTO da kasuwancin kasa da kasa; An shekara 25 babu sasancin haraji na kasa da kasa, kuma tsarin sasancin ya kwace ta yadda ’yan kalilan ne daga cikin mambobin ke sauke nauyin da ke kansu na yin komai a fili.

“WTO na matukar bukatar gyarar fuska kuma wajibi ne mutum mai asalin kwarewa ta kai tsaye a fannin ya zama wanda zai jagorance ta”, inji shi.

Da wannan kalamai, masu sharhi na ganin da wuya Babban Zauren ya cimma matsaya a kan dan takara daya babu hamayya.

Don haka, karshenta sai wakilan kasashe 164 da ke WTO sun kada kuri’a kafin a samu wanda ya yi nasara a tsakanin ’yan takarar biyan.