✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Okocha ya zama Gwarzon dan kwallon Bolton

Tsohon dan kwallon Najeriya da kuma kulob din Bolton Wanderers na Ingilla Jay-Jay Okocha ya zama Gwarzon dan kwallon kulob din a wani zabe da…

Tsohon dan kwallon Najeriya da kuma kulob din Bolton Wanderers na Ingilla Jay-Jay Okocha ya zama Gwarzon dan kwallon kulob din a wani zabe da magoya bayan kungiyar suka yi a karshen makon jiya.

Magoya bayan sun zabi Jay-Jay Okocha ne a matsayin Gwarzon dan kwallon kulob din da aka taba yi a lokacin bikin cika shekara 20 da fara amfani da katafaren filin wasansu mai suna Reebok Stadium da aka gina tun a shekarar 1997.  Sai dai a shekarar 2014 ne wani kamfani mai suna Macron ya kulla yarjejeniyar canza sunan filin wasan zuwa na Macron Stadium maimakon Reebok a wannan shekara (2017).

A lokacin bikin canza sunan filin wasan ne magoya bayan kulob din suka gudanar da zaben don zakulo Gwarzon dan kwallon kulob din tun daga kafuwarsu kawo yanzu inda Jay-Jay Okocha ya samu rinjayen kuri’u.

Okocha dai ya fafata a zaben ne da tsofaffin ’yan kwallon kulob din irin su Iban Campo na Sifen da Youri Diorkaeff na Faransa kafin ya zama Gwarzon.