A Oktobar bana sashen kyautata rayuwar al’umma da ke fadar shugaban kasa tare da hadin gwiwar PCNI da kungiyar jinkai ta Red Cross da Hukumar Agajin Gaugawa ta kasa NEMA za su shirya taron warware matsalolin da suka addabi yankin Arewa maso Gabas a karo na farko. Taron dai na da manufar jin ra’ayin dimbin jama’a wadanda ke da ra’ayi yana manufa da fahimtarsu da kungiyoyin ayyukan jinkai da injiniyoyi da masu zayyana da masana da masu kirkira da masu kafa masana’antu a yankin.
Taron sauraren fahimtar da warware matsalolin an shirya gudanar da shi cikin Oktobar 2017 zuwa Disambar 2017 kuma zai fitar da wasu tsare-tsaren ayyyukan jinkan da za su mayar da yankin cibiyar hada-hadar ayyuka. Cibiyar hada-hadar za a kafata a Yola Jihar Adamawa, inda za ta shawo kan kalubalen matsalolin da yankin ke fuskanta wadanda suka hada da wadata yankin da abinci, farfado da tattalin arziki da tsarin tarasirayar sansanin ’yan gudun hijira da bunkasa ilimi (kirkiro da dabarun shawo kan matsalolin koyon karatu) da kula da lafiya (kirkiro dabarun shawo kan matsalolin kula da lafiya kan al’amarun da suka shafi mata masu juna biyu da kananan yara da al’ummomin da ke yankin) tare da kirkiro hanyoyin kariya da za su bai wa mata da kananan yara kariya, tare da shawo kan cin zarafrin mata.
Shirin za a gudanar da shi bisa turbar da Gwamnatin Tarayya ta jajirce a kai wajen amfani fasahar kere-kere don warware matsalolin al’umma a wani shirin na Gwmanatin Buhari da ya bayar da fifiko kan kirkire-kirkire da mutane masu aiki tukuru don warware matsalolin yankin Arewa maso Gabas, yadda za a gyara tare da sake gina yankin. Don karin bayani kan wannan shirin na warware kalubalen da yankin ke fuskanta da yadda mutanen da ke da sha’awa za su shiga a dama da su, sai a bibiyin shafin sadarwar injtanet na www.nemakeathon.org.