Sakamakon kamuwar mutum 32 da cutar COVID-19 a jihar Edo, gwamna Godwin Obaseki ya wajabta wa mutane saka takunkumin rufe fuska a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin da yake wa jama’ar jihar bayani game da sake bullar cutar.
- Kyauta za a yi wa ’yan Najeriya allurar rigakafin Coronavirus — PTF
- Coronavirus ta harbi karin mutum 999, ta kashe wasu 4 a Najeriya
- COVID-19: Najeriya za ta ci tarar masu kin sa takunkumi N20,000
“Sanya takunkumi a cikin jama’a ya zama dole yanzu, kuma dole ne mutane su rage zuwa wuraren ibada, tarukan siyasa, da kuma cinkoson mutane dai ba zama dole ba.
“Mutane ka da su sake su shiga wani waje da ba su tanadar da wajen wanke hannu ba, ko kuma tanadar da sinadarin tsaftace hannu,” in ji Obaseki.
Gwamnan ya ce ya yanke shawarar yin jawabin ne saboda yadda mutanen jihar 32 suka kamu da cutar a kasa da awanni 24.
Gwamnan ya kara da cewa tun bullar cutar a karon farko, gwamnatinsa ta yi tsarin da za a gano masu dauke da cutar inda ya ce suna da manyan dakunan gwajin cutar da za su iya gwada mutane da dama a kankanin lokaci.
Kazalika, ya ce kwamitin dakile yaduwar cutar na jihar, a shirye suke don ba da kulawa ga wanda ya harbu da cutar.
Gwamna Obaseki ya ja hankalin shugabannin kasuwanni da su fadakar da ‘yan kasuwa illar cutar da kuma matakan kare kai daga ita.