Gwamnan Edo Godwin Obaseki ya ba wa fursunonin da suka tsere zuwa ranar Juma’a su mika kansu ga hukuma ko su fuskanci tsattsauran hukunci.
Gwamnan ya ba da umarnin ne yayin da yake rangadin duba wuraren da masu zanga-zangar #EndSARS suka barnata a jiharsa.
- “Kusan fursunoni 2,000 aka kubutar a gidajen yarin Edo”
- #EndSARS: An kona ofisoshin ‘yan sanda 2 da na AIT a Edo
- An sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a Edo
“Tir da irin wannan barna kuma mun san masu zanga-zangar #EndSARS za su taya mu yin Allawadai da wannan aika-aika da bata-gari suka yi.
“Mun ba wa fursunonin da suka tsere zuwa ranar Juma’a su dawo hedikwatar ’yan sanda ko su fuskacin hukunci mai tsanani idan hukuma ta cafke su”, inji Obaseki
Shugaban Hukumar Gidajen Yari a Jihar Edo, Babayo Maisadanda, ya shaida wa manema labarai cewa fursunoni 1,818 suka tsere daga gidajen yari guda biyu a jihar.
Ya ce an yi nasarar kama guda 163, sannan guda shida sun dawo da kansu.
Gwamna Obaseki ya jinjina wa Shugaba Buhari da ya ba wa sojoji damar taimaka ’yan sanda don kwantar da wutar tarzomar.