✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obasanjo ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa

Kwana biyu da sukar da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya yi wa gwamnatin shugaba Buhari yau Talata ya halarci taron tattaunawa na tsofaffin shugabanni…

Kwana biyu da sukar da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya yi wa gwamnatin shugaba Buhari yau Talata ya halarci taron tattaunawa na tsofaffin shugabanni wanda ake yi.

Obasanjo ya soki shugaban Buhari akan cewa, ‘yan Najeriya karsu sake zaben Buhari a karo na biyu a zaben watan Faburairu. Sai dai fadar shugaban kasar ta mayar masa da martani akan kalamansa

Ana saran shugabannin zasu tattauna akan biyan karancin albashi ga ma’aikata.

Wadanda suka halarci zaman taron sun hada da: Cif Ernest Shonekan, tsohon shugaban Najeriya Abdulsalam Abubakar, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da tsofaffin jojin Najeriya Mohammed Uwais, Alfa Belgore da Aloma Muktar.