✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obasanjo da Buhari sun kaurace wa taro da Jonathan

Tsofoffin shugabannin Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo da Janar Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi sun kaurace wa taron Majalisar kasa da ake…

Tsofoffin shugabannin Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo da Janar Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi sun kaurace wa taron Majalisar kasa da ake yi a fadar Shugaban kasa da ke Aso Rock. Majalisar kasar wacce ta kunshi tsofaffin shugabanni da tsofaffin manyan joji-joji da gwamnonin jihohi da shugaban Majalisar Dattawa da ta wakilai tana gudanar da taron ne a karkashin jagorancin Shugaba Goodluck Jonathan. Tsofaffin shugabannin kasa da suka hada da Janar Yakubu Gowon da Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar da kuma Cif Earnest Shonekan duk sun halarcin taron. Galibi, taron yakan mayar da hankali ne a kan batutuwan da suka shafi kasa, inda a wannan karo ya tattauna kan tsaro da kuma makomar siyasar kasar. A irin wannan taro da aka yi a watan Maris na bara ne, majalisar ta amince da yi wa tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa DSP Alams afuwa.