Shahararren dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Seatle Sounder na Amurka Obafemi Martins ya burge budurwarsa Abigail Barwuah, bayan ya sai mata mota da kudinta ya kai Naira miliyan 25.
Kamar yadda kafar sadarwa ta Pulse Nigeria ta ruwaito, dan kwallon, wanda ya dade yana soyayya da budurwar tasa Abigail ya yanke shawarar ya sai mata motar ce don ya burge ta, musamman ganin cewa kawo yanzu ta haifa masa ’ya’ya biyu ba tare da sun yi aure ba.
Abigail dai ita ce yayar shahararren dan kwallon Italiya da kulob din Liberpool na Ingila Mario Balotelli, ta yi matukar murna da kyautar da saurayinta Martins ya yi mata.
Ta bayyana farin cikinta ne a kafar sadarwa na Instagram inda ta bayyana wa duniya farin cikinta.
Sai dai Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta dade ba ta gayyaci Obafemi Martins don yi wa Najeriya kwallo ba.
Yanzu Obafemi Martins yana zaune ne a Amurka inda yake buga kwallo a kulob din Seatle Sounder a gasar rukuni-rukuni na Amurka da aka fi sani da MLS.