Ministan Wasanni da Harkokin Matasa, Sunday Dare ya sanar da bude sansanonin masu yi wa kasa hidima (NYSC) a fadin Najeriya daga ranar 10 ga watan Nuwamba.
A sakon da ya fitar a safiyar Alhamis, Ministan ya ce za a bude sansanonin NYSC din ne cikin tsauraran matakan kariyar COVID-19.
- #EndSARS: Kwamandan ’yan sanda ya tsallake rijiya da baya
- Matasa sun gudanar da zanga-zangar goyon bayan SARS a Kano
- Muna gyara tarbiyyar matasa ta hanyar hip hop —Nomiis Gee
Bude sansanonin na zuwa ne wata bakwai bayan rufe su sakamakon bullar annobar COVID-19, wadda da tilasta sanya dokar kulle da hana taruwan jama’a.
A watan Maris ne hukumar ta umarci matasa da ke rukunin farko a kashin farko na 2020 da su fara zuwa wuraren aikin da ta tura su.
A lokacin ta ce “za a gayyace su da su koma sansanin horaswa idan al’amura suka daidaita kamar yadda aka yi a shekarun baya da aka samu bullar cutar Ebola”.