Bidiyon wata sabuwar wakar Hausa da aka saki kwanan nan a shafin YouTube da sauran kafafen sada zumunta, ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu ke ganin an yi fitsara tare da bayyana tsiraici a wurare da dama a cikinsa.
Bidiyon wakar ta mawakin nan haifaffen Jihar Adamawa, Abdullahi Aliyu Shelleng wanda aka fi sani da AA Shelleng, ya fito ne tare da fitacciyar mawakiyar nan ta Jihar Legas, SlimCase.
- Rikicin Amurka: Za a fara kada kuri’ar tsige Trump
- Yadda za ku duba sakamakon jarabawar NECO 2020 cikin sauki
Wannan sabon bidiyo ya tayar da kura a zaurukan sada zumunta a yayin da wasu ke zargin ya bayyana tsiraici wanda kuma suke ganin hakan cin fuska ce ga al’adun Hausawa.
Wakar mai suna ‘North Vibes’ ta haifar da muhawara mintuna kadan bayan dora ta a kan shafin YouTube wanda kuma ta ci gaba da tashe har ta kai ga haddasa cece-kuce a zaurukan sada zumunta.
A cewar wani Tajudden Musbahu wanda ya bayyana ra’ayinsa a kan bidiyon wakar, “Wannan gaba daya ya sauka daga kan tsarin dabi’u da al’adu na Arewa.
“Cin mutunci ne ga masu magana da harshen Hausa kuma idan zan bayar da tawa shawarar, a goge wannan waka daga yanar gizo domin kuwa hakan ba daidai ba ne.”
Wani kuma cewa ya yi, “Na tabbata wannan mutumin ba daga Arewa ya fito ba, ta yaya zai yi wannan abu da harshen Hausa ba tare da an taka masa burki ba?
“Ko da yake, babu wani yare a Najeriya da zai so a danganta shi da irin wannan bidiyo.
“Kuma ni a karan kaina sai na nemi hukuma ta dauki mataki a kan wannan cin mutunci da aka yi da yaren Hausa.”