Cece-kuce ya ɓarke a Majalisar Wakilai, bayan da ɗan majalisar APC daga Jihar Eikiti, Akin Rotimi, ya goyi bayan ƙudirin dokar gyaran haraji da ake taƙaddama a kai.
Dokokin harajin guda huɗu, da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar, sun fuskanci adawa musamman daga ’yan majalisar Arewa.
A makon da ya gabata, zaman majalisar ya tattauna kan dokokin, yayin da ‘yan Arewa suka ƙi amincewa da karatun dokokin a karo na biyu.
A zaman ranar Talata, yayin gabatar da rahoto na kwamitin bunƙasa kayayyakin cikin gida, Rotimi, ya bayyana goyon bayansa kan dokar gyaran harajin.
Ya ce, “Ni ɗan Jihar Ekiti ne, jiha ta farko da ta amince gaba ɗaya da dokokin gyaran haraji a zauren majalisar wakilai.”
Wannan magana ta fusata ’yan majalisar, inda suka riƙa kururuwa domin hana shi ci gaba da magana.
Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen, ya ce, “Maganarsa ba da muhimmanci. A madadinsa, na janye maganar.”
Duk da ƙoƙarin shugaban majalisar na wanzar da zaman lafiya, ’yan majalisar sun ƙi barin Rotimi ya ci gaba da magana, wanda hakan ya tilasta shi komawa kujerarsa.
Daga baya, zaman majalisar ya mayar da hankali wajen tattauna rahotanni, inda mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Okezie Kalu, ya ci gaba da jagorantar zaman.