Majalisar Dattawa, ta kafa wani kwamiti da Sanata Abba Moro zai jagoranta domin duba matsalolin da ke cikin dokokin gyaran haraji, tare da bayar da rahoto kafin zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan dokokin.
Mataimakin Shugaban Majalisar, Barau Jibrin ne, ya sanar da hakan a zaman da aka yi a ranar Laraba.
- Bom din ’yan bindiga ya kashe fasinjoji 12 a Zamfara
- Shugaban Korea ta Kudu ya kafa dokar ta ɓaci don hukunta ƴan adawa
Barau, wanda ya jagoranci zaman, ya ce kwamitin zai yi aiki tare da Antoni Janar na Tarayya (AGF), ɓangaren zartarwa, da sauran masu ruwa da tsaki domin warware saɓanin da ake da shi a kan dokokin.
A ranar 3 ga watan Oktoban 2024, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura dokoki huɗu na gyaran haraji zuwa ga Majalisun Tarayya.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, sun gabatar da dokokin a majalisun.
Tinubu, ya bayyana cewa dokokin za su bunƙasa tsarin kuɗi a Najeriya tare da tallafa wa manufofin ci gaban gwamnatinsa.
Sai dai, ’yan Najeriya da suka haɗa da gwamnoni, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyi masu zaman kansu, da wasu ’yan majalisu sun nuna adawa da dokokin.
Barau, ya kuma sanar da sunayen Sanatoci da suka haɗa da Titus Zam (APC, Benuwe Arewa Maso Yamma), Orji Uzor Kalu (APC, Abiya ta Arewa).
Sauran sun haɗar da Sani Musa (APC, Neja ta Gabas), da Abdullahi Yahaya (APC, Kebbi ta Arewa), da sauransu, a matsayin mambobin kwamitin.