Godiya ta tabbabta ga Ubangiji Allah Mai iko duka. Barkanmu kuma da sake saduwa cikin wannan mako. A wannan mako za mu yi nazari ne a kan zama da halin kirki.
Rashin hakuri da yin fushi da halin zamba da makamantansu, sun hana mutane da dama nuna halin kirki ga juna a yau. Nuna halin kirki ga dan Adam abu ne mai sauki idan mutum na da kaunar Ubangiji Allah a cikin zuciyarsa, kamar yadda za mu a gani cikin Littafin Luka 10:27: Sai ya amsa ya ce, “Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da dukan karfinka da dukan hankalinka. Ka kuma kaunaci dan uwanka kamar kanka.”
Lallai ne idan mutum na da kaunar Allah a zuciyarsa zai so dan uwansa zai kuma nuna halin kirki ga jama’a, domin “Kauna tana sa hakuri da kirki. Kauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura. Kauna ba ta sa daga kai ko rashin kara, kauna ba ta sa son kai, ba ta jin tsokana, ba ta riko. Kauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya. Kauna tana sa daurewa a cikin kowane hali da ban-gaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali da jimiri a cikin kowane hali.”(1 Korantiyawa 13:4-7).
Ba za ka samu halin kirki a wurin da ba kauna ba, shi ya sa Littafi Mai tsarki na koya mana hanyar nuna kauna ga junanmu ta wurin kaunar Ubangiji da dukan ranmu da kuma karfinmu.
Babu shakka a cikin harkokinmu na yau da kullum mutane kan iya saba mana ta hanyoyi da dama, yakan zama da wuya mu nuna halin kirki a irin wannan hali amma idan muka dubi rayuwar Manzo Bulus cikin wasikarsa ga Ikilisiyar masu bi a Koranti; 2 Korantiya 6:4-6; “Amma ta kowace hanya muna bayyana gaskiyarmu, a kan bayin Allah muke, ta matukar jurewa da shan wahala da kuntata da masifu da shan duka da shan dauri da yawan hargitsi da yawan fama da rasa barci da kuma rasa abinci. Muna kuma bayyana gaskiyarmu ta halin tsarkaka da sani da hakuri da kirki da Ruhu Mai tsarki da sahihiyar kauna,” Ubangiji Allah zai ba mu nasara, kada mu ji tsoro ko mu dauki irin wannan tsanani ya zama mana dalilin rashin nuna kirki ga jama’a, ba haka Ubangiji Yesu Almasihu ya nuna mana ba da yana nan a duniya. Mu yi koyi da rayuwarsa, mu bi gurbin da ya nuna mana.
Idan har kana kiran kanka Kirista wato mai bin Yesu Kiristi na gaske, lallai ne fa ka zama mai bin gurbin da ya bar mana, shi ya sa ruhu mai tsarki ya bayyana mana a fili halin mutuntaka da albarkar ruhu cikin Littafi Mai tsarki don ya yi mana jagora. Yesu Almasihu ya yi zaman tsarki da kauna – har ma ga makiyansa, bai kaunaci ko nuna kirki ga almajiransa kadai ba, ya so dukan jama’a. “Sa’ar da kuwa Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karbar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa. Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce da almajiransa, “Don me malaminku yake ci tare da masu karbar haraji da masu zunubi?” Amma da Yesu ya ji haka ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya.” (Matiyu 9:10-12).
A wuri aiki, a hanya, kasuwa ko a gida kana nuna bambanci wurin yin kirki ga wani don shi ba dan uwanka ba? A rayuwarmu na yanzu za ka ga mutane na nuna bambancin kabila da na addini da jinsi da dai makamantansu, wannan ba daidai ba ne musamman idan kana kiran kanka Kirista, ta wurin nuna kirki ga mutane musamman wadanda ba sa kaunarka, rayuwarka za ta zama abin koyi a gare su har ma za su samu tsira daga irin wannan halin mugunta, domin Littafi Mai tsarki bai koya mana rama mugunta da mugunta ba. 1 Bitrus 3:9; “Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.” Idan kana cike da halin kauna da kirki Ubangiji Allah zai goya maka baya cikin duk abin da kake yi, ba zai kuma bar magabci ya ci nasara a kanka ba – don kana bin tafarkinSa.
Mafi muhimmanci shi ne rayuwa cikin ruhu, ta wurin yin haka ne za mu samu nasara a cikin rayuwar da za ta gamshi Ubangiji. Romawa 8:9: “Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba ya da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.”
Bari mu dauki lokaci mu yi nazari bisa ayoyin da muka dauko daga Littafi Mai tsarki:
Afisawa 4:31-32: “Ku rabu da kowane irin dacin rai da hasala da fushi da tankiya, da yanke da kowane irin keta. Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah Ya yafe muku ta wurin Almasihu”.
Kolosiyawa 3:12-14: “Saboda haka, sai ku dauki halin tausayi da kirki da tawali’u da salihanci da hakuri, idan ku zababbu ne na Allah, tsarkaka, kaunatattu, kuna jure wa juna, in kuma wani yana da kara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji Ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe. Fiye da wadannan duka, ku dauki halin kauna, wanda dukan kammala take kulluwa a cikinta.”
Sai mu nemi nufin Ubangiji domin jagora cikin rayuwarmu ta yau da kullum don mu nuna kaunarSa da kuma kirki ga jama’a, amin.