✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NUC ta fitar da sabon jadawalin karatun jami’a

Wata uku malaman jami'an suna yajin aiki NUC ta fitar da sabon jadawalin karatu

A yayin da malaman jami’a suka shafe kimanin wata uku suna yajin aiki, Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya (NUC), ta fitar da sabon jadawalin karatun jami’a.

Babban Sakataren Hukumar NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, ya ce wannan sabon jadawalin karatun jami’a zai taimaka wajen fito da irin abubuwan da kowace jami’a ta yi wa ’yan uwanta zarra a kansu.

Sabon jadawalin, a cewarsa, “Ya tanadi kashi 70 cikin 100 na abin ad za a koyar tare da sakamakon da ake tsammani, a yayin da jami’o’in kuma za su samar da kashi 30 cikin 100 gwargwadon abin da kowaccensu take da shi.”

Farfesa Rasheed, ya bayyana cewa sabon jadawalin (CCMAS), an tsara shi ne bayan zuzzurfan nazari kan tsohon jadawalin karatun jami’a (BMAS), kuma nan gaba kadan za a kaddamar da shi.

Ya sanar da haka ne a Abuja, a lokacin da Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya mika lasisin fara aiki ga sabbin jami’o’i 12 masu zaman kansu da suka samu sahalewar Gwamnatin Tarayya.

Ya jaddada cewa jami’o’i masu zaman kansu da suka cika sharuddan da Hukumar NUC ta gindaya ne kadai za su samu sahalewar Majalisar Zartarwar ta Tarayya.