Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta tura jami’anta kan iyakar Nijeriya da Nijar, domin samar da tsaro.
Kwamandan hukumar a Jihar Katsina, Jamilu Indabawa ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin sabon Kwanturolan Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa mai kula da shiyyar Katsina, Muhammad Umar a ofishinsa.
- Mutumin da ya ’mutu’ ya dawo bayan shekaru 8 ya ci gaba da taimakon Hamas
- Mutumin da ake zargi da yi wa ’yar shekara 2 fyade ya dora wa barasa alhaki
A cewar Indabawa, jami’an da suka tura za su yi aiki kafada-da-kafada da takwarorinsu na kwastam da ke kan iyakokin Nijeriya da Nijar yankin Jihar Katsina.
Tun da farko, sabon kwanturolan kwastam da aka tura Muhammad Umar ya ce ya kai ziyarar ce domin kara yaukaka alakar aiki tsakanin hukumomin biyu.
“Hukumar mu ta hana fasa kwauri ba za ta iya aiki ita kadai ba saboda fadin iyakar Katsina da Nijar.”
“Sibil Difens za su iya taimaka mana duba da cewa sun dade a kusan kowanne sashi na Jihar Katsina,” in ji Muhammad Umar.