Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ta ce jami’anta sun kwace motoci 300 da ake amfani da su a haramtattun matatun mai a sassan Najeriya.
Babban Kwamandan NSCDC, Ahmed Abubakar Audi ya ce hukumar ta lalata haramtattun matatun mai 50 tare da cafke mutum 200 a bisa alaka da matatun a chikin shekara guda.
- Yoyon fitsari: Za a yi wa mata 150 aiki kyauta da tallafi a Kano
- Buhari da Gwamnoni sun halarci daurin auren dan Sarkin Kano a Sakkwato
“Matsalar satar mai da fasa bututan mai na karuwa, amma muna kokarin shawo kanta shi ya sa muka kira wannan taro domin lalubo mafita,“ inji shi bayan wani taro da kwamandojin hukumar.
Ya yi bayanin ne bayan zaman da ja jagoranci kwamandojin hukumar da shugabannin sashen yaki da fasa butuun mai domin tsara yadda za a magance matsalar a fadin Najeriya.
Ya ce hukumarsa ta fara gudanar da wani binciken sirri kan rundunarta ta yaki da ayyukan satar mai da fasa bututu a fadin Najeriya.