✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Noman Zabibi zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya’

Buhun zabibi idan aka busar ana samunsa daga Naira dubu tara zuwa dubu 10.

Kamar citta da sauran kayayyakin noma, Zabibi (Tumeric) ko kuma Kurkur kamar yadda wadansu ke kira a wasu sassa, daya ne daga cikin kayan gona da ake nomawa a Kudancin Kaduna.

Zabibi yana tafiya kafada-dakafada ne da citta domin dukkansu akan noma su ne a farko ko tsakiyar watan Afrilu kuma a fara girbewa a lokaci guda.

Kamar yadda kananan hukumomin Kachiya da Kagarko da Jaba da Jama’a suka shahara a noman citta a Jihar Kaduna, haka su ne kan gaba wajen noman Zabibi, inda ake safararsa zuwa jihohin Legas da Kano da Sakkwato.

Binciken kimiyya ya tabbatar da amfanin Zabibi da akan sarrafa shi don kiwon lafiya daga matsalolin da suka shafi cututtukan kwakwalwa da na jiki da suka hada da ciwon zuciya da na kansa da na fatar jiki da dukkan cututtukan da kwayoyin bakteriya (masu yaduwa) da fungus suke haifarwa, sakamakon sinadarin ‘Curcumin’ da ke kunshe a cikin Zabibin.

Malam Yusha’u Dayyabu, daya daga cikin masu noman Zabibi a Karamar Hukumar Jama’a, ya shaida wa Aminiya cewa, noman Zabibi ba ya da wahala kamar noman citta, inda manomi yake bukatar iri da wurin shuka sai maganin feshi da takin gargajiya.

“Ba a sa wa Zabibi takin zamani sai kashin dabbobi kamar na shanu da tumaki da awaki da na kaji.

“Da zarar mutum ya noma Zabibi a lokacin zai yi feshin maganin ciyayi domin tsironsa ba ya son magani don yana iya mutuwa nan take.

“Idan ya fito da sauran ciyayi sai dai a yi ciro ba dama a sake yin feshi a gonar,” inji shi.

Ya ce, idan an shuka Zabibi a gona sau daya za a iya girbewa a shekara hudu tana ci gaba da tsira ba tare da an sake shukawa ba.

Ya ce bayan cire Zabibi idan ya yi, akan wanke a yayyanka, yayin da wadansu sukan yayyanka shi ba tare da wankewa ba daga nan sai a shanya shi ya bushe kafin a mayar cikin buhunhuna a sayar wa daidaikun mutane da kamfanonin da ke fitar da shi zuwa kasashen waje ko a kai jihohin Sakkwato da Kano da Legas.

“Turawan Jamus da mutanen kasar Indiya suka fi zuwa sayen Zabibi a yanzu domin suna sarrafa shi a abubuwa da dama da suka hada da sa shi a cikin magunguna saboda amfaninsa a jikin dan Adam kamar yadda binciken kimiyya ya gano.

“Mu dai a nan kasar an fi amfani da shi wajen sa sinadarinsa a magi da kori da magani da kuma jimar fatu.

“Sannan ana amfani da shi wajen yin dilka idan an hada shi da citta da mata kan shafa kafin su yi wanka don gyaran fatarsu, kamar yadda suke yin hodar kurkur suna shafawa a fuska.

“A nan za ka ga muna dakawa ko nikawa ana sayarwa don amfanin gida domin mukan sa a cikin ruwan shayi ko mu hada da zuma muna sha don maganin wasu cututtuka a gargajiyance da suka hada da hawan jini ko ciwon sukari ko kasala ko yawan maiko a jiki da sauransu,” inji shi.

Da yake bayani a kan kasuwancin Zabibi, Yusha’u ya ce, a yanzu ba a samun tsohon Zabibi sai kadan domin lokacin fitowar sabon ne yanzu sai dai da za a samu kowane buhu daya na busasshen tsohon Zabibin za a saye shi a kan Naira dubu 30 zuwa dubu 35.

Ya ce, “Amma yanzu danyensa tunda yana kan fitowa ke nan akan sayi buhun a kan Naira dubu biyar, ko kasa da haka ko sama da haka har zuwa dubu shida.

“Shi kuma sabon da aka yanko aka busar ana samunsa daga Naira dubu tara zuwa dubu 10.”

A karshe Malam Yusha’u ya bukaci Gwamnatin Jihar Kaduna ta Tarayya da sauran masu ruwa- da-tsaki a harkokin noma da kungiyoyi su rika ba su tallafi don bunkasa harkar noman Zabibi a Najeriya ganin yadda bukatarsa ke karuwa a duniya domin amfaninsa da ake ta ganowa da kuma bunkasarsa.

“Gwamnati za ta amfana sosai idan ta taimaka wa manoma kuma hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan dogaro da kai ga ’yan kasa kuma zai sa a rika bude kamfanonin sarrafa shi a cikin kasa.

“Ba lallai sai kayan abinci ne kawai ko manoma kayan abinci ne gwamnati za ta tallafawa ba, har ma da masu noman sauran kayan gona da suka hada da citta da Zabibi da sauransu, domin baya ga taimakon ’yan kasa, ita ma gwamnatin za ta amfana ta hanyoyi daban-daban da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki.”