Gwamnatin Katsina na shirin kashe Naira biliyan 1.8 wurin gyara da kuma fadada madatsar ruwa ta Sulma da ke Karamar Hukumar Kafur, a kokarinta na bunkasa noman rani a Jihar.
Mashawarcin Gwamnan Jihar Katsina kan Harkokin Noma da Albarkatun Kasa, Abba Abdalla, ne ya sanar da haka, inda ya ce Gwamnatin Jihar za ta kara gina kasuwannin amfanin gona a lokacin rani domin kara wa manoma kwarin gwiwa.
- ‘Tun ina shekara bakwai mahaifina yake kwanciya da ni’
- Tafsirin Ramadan: Izala ta tura malamai 500 zuwa kasashe
- Abin da ya sa aka umarci jihohi su dakatar da yin rigakafin COVID-19
- Dalilai uku na sauke Sufeto Janar Mohammed Adamu
“Aikin Madatsar Ruwa ta Salma zai taimaka wajen bunkasa harkokin noma da tattalin arziki.
“Gwamnatin Jihar ta kuma gina wurin busarwa da adana amfanin gona irin su tumatir da albasa da barkono da sauransu,” inji shi.
A shekarar 2019 Majalisar Dokokin Jihar Katsina, ta amince da aikin gyara da fadada madatsar ruwa ta Sulma tare da gina masa titi.
Aikin ya kuma kunshi gidan tashar samar da wutar lantarki mai karfin kilowat 80.