Jam’iyyar NNPP ta yi Allah-wadai da yunkurin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na karbo wani sabon bashi na Naira biliyan 10 daga Bankin Access da nufin gudanar da aikin sanya naurar tsaro ta CCTV a fadin jihar.
Wannan bayani ya fito ne daga Shugaban Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, Honorabul Haruna Umar Doguwar.
- Za a hana amfani da kananzir da icen girki a Najeriya
- Cikar wa’adin INEC: APC ta zabi Kabiru Masari a matsayin mataimakin Tinubu na wucin gadi
Ya ce ba zai yiwu Jam’iyyar NNPP ta nade hannu ta zuba ido wannan gwamnati tana lafta wa jihar bashi ba tare da yin wasu ayyuka a kasa ba.
“Za a iya cewa Gwamna Ganduje yana amfani da kujerarsa yana lalata cigaban jihar da kuma na yayanmu.
“Saboda lalacewa irin ta Gwamnatin Ganduje ta gaza biya wa daliban makarantun sakandiare kudin jarrabawa, lamarin da ya tilasta dalibai da yawa daina karatun inda kuma wasu suke kokarin dainawa.
“Duk da irin matsalar ruwa da ta addabi jama’ar jihar, Gwamna Ganduje ya kawar da kansa a kai inda ya tafi neman kudin da zai yi wani aiki da bai kai wadannan muhimmanci ba, wato na sanya naurar tsaro ta CCTV.
“Idan za a iya tunawa a baya dan takararmu da muke fatan ya zama shugaban kasa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanya irin wannan na’ura a wasu muhimman wurare na jihar nan.
“Sai ga shi wannan gwamnatin ta gaza kula da su har tana kokarin karbo bashin Naira Biliyan 10 don sanya sabbi.
“Mutanen Kano ba za su amince wa Gwamna ya karbi bashin da zai iya jefa rayuwarsu cikin wani hali.”
A cewarsa jam’iyyar ta NNPP tana kira ga Majalisar Dokoki ta bijire tare da kin yarda da ire-iren wadannan bukatu na gwamnan.
“Muna kira ga ’yan majalisa da su sanya bukatun al’ummar Jihar Kano a gaban bukatar son zuciya na gwamnan, kafin mu zo mu karbe mulki a zaben 2023.
“Haka kuma muna kiran Bankin Access da ya cire hannu daga bayar da bashin ga gwamnan wanda yake son jefa a’lummar jihar cikin wani hali saboda bukatun son ransa.
“Muna da yakinin za a karbi wannan bashin ne don a lullube badakalar da aka tafka da lalitar jihar a lokacin zabukan fidda gwani.
“Na tabbata mutanen Kano ba za su manta da bashin Naira biliyan 15 da gwamnan ya karbo da niyyar gyara harkar ilimi wanda kuma aka karkatar da kudin zuwa wani abu na daban, inda kuma a karshe yara da dama sun daina zuwa makaranta sakamakon gwamnati ta gaza biya musu kudin jarrabawa a matakin kammala firamare da kuma na kammala sakandare.”