Jam’iyyar NNPP ta bukaci Hukumar Tsaro ta DSS ta sako mamboninta shida da ta tsare a Karamar Hukuamr Birni da kuma Madobi a Jihar Kano.
Madobi ita ce karamar hukumar da dan takarar shugaban kasa na NNPP, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya fito.
- Gwamnatin Kano ta zargi NNPP da shirya magudi a zaben gwamna
- An kashe mutum 4 a rikicin jami’an tsaro da ’yan Shi’a a Kaduna
Jigo a jami’iyyar a Kano, Bappa Bichi, wanda ya yi zargin hannun Daraktan DSS na jihar wajen kuntata wa jam’iyyar, ya ce a cikin daren ranar Laraba jami’an hukumar suka kama mambobin jam’iyyar suka tafi da su.
“Wannan na cikin miyagun dalilan barin Daraktan DSS ya ci gaba da zama a ofis — alhalin lokacin ritayarsa ya dade da yi—; tsare jagororin jam’iyya, tsrora magoya baya, hana su zabe, da samar da damar yin magudin zabe,” in ji shi ga wani taron ’yan jarida ranar Alhamis a Kano, kamar yadda kamfanin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Wadanda aka kama a cewarsa su ne Suyudi Hassan, Sama’ila Hausawa, Alhaji Muhammadu Hausawa, Alhaji Habibu, Habu Tabule da kuma Malam Sama’ila Mangu.
Aminiya ta ruwaito a ranar Alhamis cewa kotun Majistare da ke zamanta a No-Man’s Land a Kano ta ba wa DSS izinin ci gaba da tsare Habu Tabule da Sama’ila Mangu na tsawon mako biyar, bayan hukumar ta gurfanar da su kan yada kalaman tunzuri a kafofin sada zumunta.
Amma Baffa Bichi ya bukaci a gudanar da cikakken bincike kan take-taken wasu mabobin jam’iyyar APC mai mulkin jihar na tayar da rikici da tunzuri gabanin zaben gwamnonin da ’yan majalisar jiha na ranar Asabar.
Jam’iyyar, ya ce ta yi hakan ne bayan samun wasika daga rundunar ’yan sanda da ke umartar daukacin jam’iyyun siyasa da su dakatar da duk wani zanga-zangar lumana ko gangamin yakin neman zabe ko tattakin siyasa.
“Mun janye ne saboda kimar Mataimakin Shugaban ’Yan Sanda Mai Kula da Shiyya ta 1.