✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abba Kabir Yusuf na NNPP na shirin zama Gwamnan Kano

INEC za ta sanar da sakamakon a hukumance nan gaba

Dan takarar Jam’iyyar adawa ta NNPP a Jihar Kano, Abba Kabir Yusufu, ya zama zababben gwamnan jihar, bisa dukkan alamu.

Bayan tattara sakamakon kananan hukumomi 44 na zaben, Abba ya yi wa abokin fafatawarsa na APC kuma mataimakin gwamna mai ci, Nasir Yusuf Gawuna fininkau da tazarar kuri’u 128,897.

Tuni dai magoya bayan NNPP suka fara murna, yayin da ake jiran sanarwa a hukumance daga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Abba a mastayin zababben gwamna.

A halin yanzu dai INEC ta dage sanarwar karshen zuwa nan awa biyu masu zuwa.

Kafin nan, sai da baturen zaben INEC na Jihar Kano, Ahmad Doko Ibrahim, ya nuna wa wakilan jam’iyyu da ‘yan jarida da masu sa ido da ke wurin takardun tattara sakamakon na karshe domin su tabbatar da cewa babu wani rubutu a cikin takardun.