✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPP na shirin amfani da kuɗaɗen ƙananan hukumomi a zaɓen Kano —APC

Abdullahi Abbas ya zargi gwamnatin jihar da neman amfani da kuɗaɗen ƙananan hukumomin wajen ɗaukar nauyin wasu ’yan takarar NNPP a zaɓen

Jam’iyyar APC na zargin Gwamnatin NNPP a Jihar Kano da yunƙurin karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi domin gudanar da zaɓensu da ke tafe.

Shugaban APC a Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar tana ƙoƙarin karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi domin ɗaukar nauyin ’yan takarar NNPP a zaɓen.

Abdullahi Abbas ya bukaci Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙin Kasa (EFCC) da takwararta ICPC su sanya ido sosai a kan ma’aikatar ƙananan hukumomin jihar game da wannan lamari.

“Muna sanar da EFCC da ICPC cewa bayan rushe shugabannin riƙon ƙananan hukumomi, ma’aikatar tana ƙoƙarin amfani da Daraktocin Kula da Ma’aikata, waɗanda ma’aikatan gwamnati ne da ke da alhakin kula da kuɗaɗe, da zummar amfani da kuɗaɗen al’umma wajen gudanar da zaɓen.

“Ya kamata EFCC ta binciki asusun ƙananan hukumomi 44 da ke Jihar Kano domin tabbatar da ba a karkatar da kuɗaɗensu ba,” in ji Abdullahi Abbas.

Ya ƙara da neman EFCC ta gayyaci shugabannin riƙon ƙananan hukumomin jihar da aka rushe, kowanensu ya bayar da bayanan kuɗaɗen da ya bari.

Su kuma Daraktocin Kula da Ma’aikatan da aka miƙa wa ragama su kawo bayanan yadda suka sarrafa kuɗaɗen da suka gada daga shugabannin riƙon, domin daƙile karkatar da su wajen zuwa zaɓen ƙananan hukumomin.

Ya ce hakan na da muhimmanci, la’akari da zargin da ake wa tsohon gwamnan jihar kuma jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na karkatar da Naira biliyan 30.8 daga asusun ƙananan hukumomi domin zaben shugaban ƙasa a shekarar 2015.