Jam’iyyar NNPP da PDP a Jihar Jigawa, sun warware matsalolinsu na cikin gida, domin shiga zaɓen kananan hukumomi da ke tafe a jihar.
NNPP dai ta fuskanci cece-kuce game da zaɓen ’yan takararta na shugaban ƙanana hukumomi, amma shugaban jam’iyyar a jihar, Mutari Ibrahim Gonga, ya bayyana cewa an warware matsalar.
Jam’iyyar ta gudanar da zaɓen fidda gwaninta ne a ƙaramar hukumar Birnin Kudu, wanda a baya aka samu saɓani, inda aka tabbatar da Saleh Adamu Aliyu a matsayin halastaccen ɗan takara.
Jam’iyyar adawa ta PDP a nata ɓangaren, ta rubuta wa Hukumar Zaɓe ta jihar (SIEC), cewa ta rage kuɗin fom ɗin takarar shugaban ƙaramar hukuma da na kansiloli.
Hukumar zaɓen ta sanya Naira miliyan biyae a matsayin kuɗin fom na shugaban ƙaramar hukuma da Naira miliyan biyu na kujerun kansiloli.
Jam’iyyar ta kuma umarci ’yan takararta da za su iya ɗaukar nauyin kansu a zaɓen da su yi.
Ya zuwa yanzu dai ’yan takara 15 ne masu neman shugabancin ƙananan hukumomi da kansiloli suka sayi fom don shiga zaɓen.
Ƙananan hukumomin da ’yan PDP suka sayi fom ɗin sun haɗa da Dutse, Birnin-Kudu da Kiyawa da Gwaram da Jahun da Hadejia da Miga da Kafin-Hausa.
Ragowar sun haɗa da Kaugama da Malam-Madori da Guru da Garki da Taura da Ringim da Sule-tankarkar.
Kazalika, sauran ƙananan hukumomin dai na ci gaba da tattaunawa kan yadda za su shiga zaɓen.
An shirya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin a ranar 5 ga watan Oktoba, 2024.