Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya yi asarar naira biliyan 9.5 a hada-hadar mai da iskar gas da ya yi cikin watan Maris, 2020.
NNPC ya ce asarar ta kai kashi 300 kasancewar an sayar da albarkatun mai na Dala miliyan 256.19 a watan Maris, 2020, wanda ke nufin an rasa kashi 30.89, sabanin ribar biliyan N3.95 da aka samu a watan Fabrairu.
Rahoton kamfanin kan kudade da ayyukansa na watan Maris ya ce hakan ta faru ne musamman saboda asarar kashi 181 da aka samu a wasu kamfanonin NNPC saboda faduwar farashin mai, sakamakon cutar COVID-19 da ta rage zirga-zirga da yin amfani da mai da dangoginsa.
- NNPC ya yi nisa da aikin neman danyen mai a Filato
- Mai faci ya saci kamfan wata mata zai yi tsafin kudi
Kamfanonin sun hada National Oil Company’s Upstream Subsidiary, da kuma Nigerian Petroleum Development Company’s (NPDC).
Ya kara da cewa a hada-hadar da aka gudanar kacokan, an samu Dala miliyan 184.59 (kashi 72.05) daga danyen mai, akasin Dala miliyan 281.14 da aka samu a Fabrairu, sai kuma iskar gas da aka sayar na Dala miliyan 71.60.
Ya ce, daga watan Maris, 2019 zuwa Maris na 2020, danyen mai da iskar gas da aka kai kasashen waje ya haura Dala miliyan 4.95.