✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPC ta musanta kara kudin aikin bututun iskar gas

NNPC ya yi kurarin kai karar kafar da ta zarge shi da kara kudin aikin bututun iskar gas

Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya karyata rahoton da ke cewa ya yi karin kudin aikin gina bututun iskar gas na AJaokutu-Kaduna-Kano, zuwa Dala biliyan 1.527.

NNPC wanda ya ce zargin ba shi da tushe, ya yi barazanar maka kafar intanet da ta yada labarin na kanzon kuregen a gaban kuliya.

Daraktan Hulda da Jama’a na NNPC, Kennie Obateru, ya ce kamfanin ya ankarar da hukumar kula da sayayya ta gwamanti (BPP) game da zargin, kuma hukumar ta musanta shi a matsayin mara tushe.

“A bayyane yake cewa an kirkiri sharhin ne domin goga wa Shugaban NNPC Malam Mele Kolo Kyari da kuma BPP kashin kaji.

“Malama Mele Kyare bai zama Shugaban NNPC ba sai a watan Yulin 2019, amma jaridar ta ce yana da hannu a abin da aka yi a 2017.

“Abin takaici ne da take cewa rage Dala miliyan 300 a kudin aikin da aka yi an yi ne a wa’adin mulkin Kyari tare da amcincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya”.

NNPC ta ce bayar da aikin AKK ya bi dukkannin ka’idoji kuma a bayyane wanda ya kai ga bayar da kwangilar, don haka ya yi mamakin zargin kara kudin aikin da ake masa.

“Dukkannin hukumomin da abun ya shafa sai da aka samu amincewarsu.

“Wannan yunkuri ne da gangan na rudar da ‘yan Najeriya da abin da ba shi da tushe”, inji sanarwar.

NNPC ya ce aikin bututun gas na AKK na daga cikin manyan ayyukan da aka gudanar da tsarin bayar da shi ta hanyar yin komai a fili tare da cika dukkannin ka’idoji.