Kamfanin NNPC ya ba da tabbacin cewa zuwa karshen shekarar 2024 za a kammala aikin bututun iskar gas da ya tashi daga Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK).
Shugaban Rukuncin Kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya ce bututun iskar gas din wanda aka kammala kashi 80 cikin 100 zai kara sada yankin Arewa da Neja Delta da ma sauran sassan Najeriya.
- Matatar Man Kaduna za ta fara aiki a 2024 —Minista
- Rikicin Gaza: Ƙasar Falasɗinawa mai cikakken ’yanci ce mafitar —Najeriya
Mele Kyari ya bayyana haka ne ta bakin mataimakinsa mai kula da bangaren Iskar Gas da Makamashin Zamani, Olalekan Ogunleye, a yayin rangadin bangaren aikin da aka kammala a yankin Kogin Hadejia.
Olalekan ya ce, “za mu ci gaba da bayar da muhimmanci ga kammala aiki a kan lokaci, don haka tilas mu kara hada karfi da karfe wajen tabbatar da an kammala wannan aiki mai muhimmanci ga habaka tattalin arzikin Najeriya.”
Ya kuma yaba wa kamfanin BRENTEXCCP Limited da aka ba wa aikin shimfida bututun iskar gas din, ganin cewa kawo yanzu ba a samu rauni ko asarar rai ba a tsawon awa miliyan 7.2 da daukacin ma’aikata suka shafe a kansa.
Mataimakin shugabna kamfanin na BRENTEXCCP Limited, Sani Abubakar, ya ba da tabbacin cewa za a kammala shimfida bututun iskar gas din kafin cikar wa’adin da gwamnati ta ba su, domin duk abubuwan da ake bukata na aikin suna kasa.