Kamfanin mai na Kasa NNPCL ya tallata matatar mai ta garin Fatakwal da ta fara aiki ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu wadanda za su tafiyar da ita yadda ya dace.
Ana iya tuna cewa Gwamnatin Tarayya ta ce matatar za ta fara aiki gadan-gadan cikin watanni hudun farkon wannan shekara.
- Kotun Koli ta jingine yanke hukunci kan Zaben Gwamnan Nasarawa
- Za a raba wa manoma injin ban ruwa mai aiki da hasken rana a Kebbi
A halin yanzu dai, ana sa ran matatar za ta fara da tace ganga dubu 60 a kowacce rana kafin daga bisani a fara tace ganga dubu 210 kowacce rana.
NNPCL a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya ce akwai bukatar bai wa ‘yan kasuwa masu sha’awa damar gwada basirarsu wajen tafiyar da matatar don tabbatar da zamanta da kafafuwanta ba tare da samun wata matsala ba.
Sai dai kuma kamfanin ya ce duk dan kasuwar da ke bukatar karbar wannan matata sai ya nuna shaidar samun ribar akalla dala biliyan biyu tun daga shekarar 2019 a matsayin shaidar cewa shi dan kasuwa ne cikakke.
NNPCL ya ce a ranar 4 ga watan Janairu zai kammala gwaje-gwaje a matatar man ta Fatakwal, abinda ke nufin a yanzu fara aiki ne kawai ya rage.
Matatar man ta Fatakwal da aka rufe shekaru biyar da suka gabata na daga cikin matatun mai na gwamnati da aka shafe shekaru ana tafka muhawara a kansu, amma gwamnatin Najeriya na kokarin farfado da su domin kawo karshen dogaron da kasar ke yi kan kayayyakin da aka tace daga kasashen waje.
Ana dai ganin nuna halin ko in kula na gwamnatocin baya ne ya kashe manyan matatun biyu da kasar ke da su, yayin da siyasa ta dabaibaye gyaran su, duk da alkawarin yin hakan da kowacce gwamnati ke yi a lokutan yakin neman zabe.