✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Nnamdi Kanu ya musanta zargin daukar nauyin ta’addanci

Lauyan Kanu ya ce duk tuhume-tuhumen ba su da tushe balle makama.

Jagoran Kungiyar ‘Yan Awaren Biyafara, Nnamdi Kanu ya musanta zargin daukar nauyin ta’addanci da cin amanar kasa a gaban kotu da gwamnatin tarayya ke masa.

Kanu ya gurfana a gaban kotu a ranar Laraba, inda ake tuhumarsa kan sabbin laifuka 16, sai dai ya musanta aikata daya daga cikin laifukan da ake tuhumarsa.

Lauyan mai shigar da kara, Labaran Magaji, ya sanar da kotu za ta iya yanke hukunci sakamakon gabatar da shaidunsa biyu da ya yi.

Ya bayar da misali da sashe na 396 na kundin laifuka na 2015 wanda ya tanadi cewa a fara shari’a bayan an gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya.

Sai dai lauyan Kanu, Mike Ozekhome (SAN) ya ce ba za a iya ci gaba da shari’ar ba saboda yana da wasu kararraki guda biyu, daya na kalubalantar cancantar tuhumar da ake yi masa, daya kuma na rashin yi masa adalci.

Ya kuma kara da cewa tuhume-tuhumen da ake yi wa Kanu ba su da tushe balle makama, kuma ba su da karfin doka, lamarin da ya ce laifukan da ake zargin wanda ake tuhumar an aikata su ne a kasar Ingila ba a Najeriya ba.

Da ta ke yanke hukunci, Mai Shari’a Binta Nyako, ta ce sai an gabatar kwararan hujojji kafin ta zartar da hukunci kan wanda ake zargi.

Nyako ta sanya ranar 16 ga watan Fabrairu, 2022 ga lauyoyin kowane bangare don gabatar da hujojji masu karfi da za su taimaka wa shari’ar.

Sannan ta ba da umarnin ci gaba da tsare Kanu karkashin kulawar rundunar tsaro ta DSS.

A halin yanzu, lauyan gwamnatin tarayya, Magaji ya shaida wa kotu cewa Hukumar DSS ta bai wa Kanu katifa, matashin kai, barguna da dai sauransu domin bin umarnin kotu.