Zauren sada zumunta na Facebook ya goge shafin shugaban ’yan awaren IPOB masu fafutikar kafa yankin Biyafara IPOB, Nnamdi Kanu, bayan sakin wani hoton bidiyo inda ya zargi Fulani makiyaya da lalata gonaki.
Lamarin na zuwa ne a yayin da Najeriya ke fama da rikicin makiyaya da manoma a yankuna daban-daban na kasar.
- An girke jami’an tsaro a gidan Sheikh Abduljabbar
- Mutum 4 sun rasu a hadarin mota a Oyo
- Rufe masallaci: Sheikh Abduljabbar ya yi raddi ga Gwamnatin Kano
Hoton bidiyon da Nnamdi Kanu ya wallafa ya nuna wasu mutane da ake zargi mambobin wata kungiyar sa kai ce a Kudu maso Gabashin Najeriya mai suna Eastern Security Network, wadanda ke faman kashe shanu a wuraren zaman Fulani makiyaya.
A wata sanarwa da Kakakin Facebook ya yi da BBC ya bayyana cewa, daya daga cikin burace-buracen kamfanin shi ne bai wa mutane dama su fadi ra’ayoyinsu tare da sanin cewa za su samu wani tsaro yayin amfani da shafin.
Sanarwar ta ce an goge shafin Nnamdi Kanu saboda tanadin wasu dokoki na dakile sakonnin da aka wallafa masu dauke da kalaman batanci da masu tayar da husuma da zauren na Facebook ya yi.
Wani dan kungiyar Eastern Security Network ya ce za su duk waya mai yiwuwa a kan lamarin goge shafin jagoran nasu a yayin da haramcin bai shafi Radio Biafra ba da sauran shafukan dandalan sada zumunta na kungiyar.
Shafin Nnamdi Kanu na Facebook ya kasance wani dandali na ’yan awaren IPOB da ke duk wani kwararo da sako a fadin duniya.
Ana iya tuna cewa a shekarar 2017 ne gwamnatin Najeriya ta bayyana haramci a kan dukkanin ayyukan kungiyar IPOB sannan ta ayyanata a matsayin kungiyar ta’addanci.