Kungiyar likitoci ta Najeriya NMA reshen jihar Ondo ta bukaci gwamnatin jihar da ta magance kalubalen tsaro ta hanyar karuwar garkuwa da jama’a da kisan gillar da ake yi a jihar.
Shugaban kungiyar NMA na jihar Dakta Olawale Oke ne ya yi kiran yau Litinin a Akure babban birnin jihar lokacin da yake ganawa da manema labarai.
Kungiyar ta nuna rashin jin dadinta game da yin garkuwa da wasu ‘yan bindiga suka yi wa wasu masu ciki da wasu ma’aikatan asibiti da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa dasu a hanyar Akure zuwa garin Owo ranar Alhamis.